www.sautizallah.com
Legit - Purevybz Pressplay

Ahmed Musa Zai Gina Makaranta A Jos

Kaftin din kungiyar kwallon kafa Super Eagles ta Najeriya,

0

Ahmed Musa ya ce zai gina makarantar ce a yankin Bukuru da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu, inda a nan ne ya taso domin kyautatawa al’ummar yankin.

Shahararen dan kwallon kafar ya bayyana haka ne a shafinsa na Instagram, inda ya ce “Ba zan manta da unguwarmu ba da kuma gudunmawar da ya kamata na yi wa al’ummarta.

 

“Don haka nake murnar sanar da fara aikin gina makarantar M&S a Jihar Filato a Karamar Hukumar Jos ta Kudu a garin Bukuru, domin ilimi mabudi ne,” inji shi.

Ahmed wanda dan asalin Jihar Filato ne ya buga wa kungiyoyi da dama wasa a ciki da wajen Najeriya.

Tushe: Aminiya

Leave a Reply