Labarai

An ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, ma’aikatar ta ce bayan wani rahoto da suka samu na sirri dakarunta sun yi nasarar ceto mutanen tare da kashe wani dan bindiga guda.

Sanarwar ta ce tuni aka sake mayar da mutanen ga iyalansu, tun a ranar 7 ga watan Janairu da aka kuɓutar da su.

Sanarwar ta ƙara da cewa ma’aikatar tsaron ba za ta kyale wasu ɓata gari su riƙa cin karensu babu babbaka ba a fadin ƙasar, za ta yi iya yinta domin hana hakan faruwa a ko ina cikin kasar.

Tushe: BBC

Kindly follow our social handles below for latest update and more;

Facebook Page: @Sautizallah
Instagram: @Sautizallah
YouTube: Sautizallah TV
Twitter: @Sautizallah

Thanks

Leave a Reply