www.sautizallah.com
Legit - Purevybz Pressplay

An kama masu yi wa ƴan fashin daji safarar makamai

0

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta tabbatar da kama wasu masu safarar makamai ga ƴan fashin daji da masu garkuwa da jama’a a jihar.

Mai magana da yawun rundunar SP Gambo Isah ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, inda ya ce da farko an kama wani mutumi mai shekaru 35 da aka jima ana zargin yana kai wa yan fashin dajin makamai.

Ya ce bayanan sirrin da rundunar ta samu a kan mutumin mai suna Lawan Zayyanu da ke zaune a ƙauyen Maduro ne suka sanya aka kama shi domin gudanar da bincike game da zargin da ake yi masa.

SP Gambo Isah ya ƙara da cewa ya bayyana musu cewa akwai wani mai gidansa Haruna Yusuf da ke zaune a ƙaramar hukumar Kaita, wanda kuma da shi ne suke wannan harka.

Ya ce lokacin da aka je gidansa an tarar da wasu ramuka da ya hahhaƙa a gefen gidansa, waɗanda yake amfani da su wajen ɓoye makaman da ake kai masa.

Rundunar ta ƙara da cewa ta kama ƙarin wasu mutane biyu da suke haɗa baki da waɗannan mutane domin shigo da makaman, da kuma raba su ga ƴan fashin daji a wasu sassan jihar ta Katsina.

Tarin makaman da aka gano hannun mutumin

SP Gambo Isah ya shaida wa manema labarai cewa a yayin samamen jami’ansu sun gano wasu tarin makamai da ko dai mutanen ke amfani da su, ko kuma waɗanda ba a kai ga kai wa yan fashin dajin bane.

Ya ce makaman sun hadar da manyan bindigu guda biyu, da kuma wasu da ake iya girkewa a ƙasa guda biyu, da alburusan kakkaɓo jirgin sama har guda dari da sittin a tare da su.

Ya ƙara da cewa an kuma gano wasu tsabar kuɗi da suka haɗar da Sefa ta Jamhuriyyar Nijar kusan miliyan uku, baya ga wasu tarin kuɗin samfurin naira ta Najeriya su ma da yawa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsinan ya tabbatar da cewa bincikensu ya gano cewa mutumin da ke jagorantar masu safarar miyagun makaman ɗan Jamhuriyyar Nijar ne ba Najeriya ba.

Ita dai jihar Katsina ta jima tana fama da matsalar tsaro, kana an jima ana jefa ayar tambaya kan yadda yan bindiga ke samun makaman da suke amfani da su wajen kai hare-hare.

Tushe: BBC Hausa
Kindly follow our social handles below for latest update and more;

Facebook Page: @Sautizallah
Instagram: @Sautizallah
YouTube: Sautizallah TV
Twitter: @Sautizallah

Thanks

Leave a Reply