www.sautizallah.com
Legit - Purevybz Pressplay

Boko Haram: Ta kai Hari Gaidam tare da sace hakimi

Rundunar ƴan sandan jihar Yobe da ake arewa maso gabashin Najeriya

0

Kakakin rundunar ƴan sandan ASP Dungus Abdulkareem ya shaida wa BBC cewa da misalin karfe daya na ranar jiya ne, aka fara raɗe-raɗin cewa an ga mayaƙan Boko Haram a bayan gari da motoci 11, da hakan ya sa mutanen gari suka fara guje-guje.

Daga nan ne jami’an tsaro suka fara ɗaura ɗamarar shirin ko-ta-kwana, amma daga bisani aka bayyana cewa labarin ba gaskiya ba ne, don haka jama’a suka sakankance suka shiga harkokinsu.

”Wadannan mahara sun shigo cikin garin Gaidam da kafafunsu, suka bar motocinsu a bayan gari, saboda sun fahimci cewar jami’an tsaro sun samu labari – da suka shigo sai daf da magariba suka fara harbe-harbe,” in ji ASP Dungus.

 

Ya kuma ƙara da cewa, sun yi awon gaba da Lawanin (hakimi) ƙauyen Ma-Gana, kana suka ƙona gidan tsohon shugaban ƙaramar hukumar ta Gaidam ƙurmus, suka kuma lalata gidan Lawanin da suka sace.

”Sun kuma farfasa shagunan sayar da magunguna suka kwasa, suka fasa shagunan kayan abinci suka kwasa, sun kuma ƙona wasu shagunan kafin su shiga babban asibitin garin suka kwashi magunguna a can,” ya ce.

Rundunar ƴan sandan in ji ta bakin kakakin nata, ta bayyana cewa akwai wata karamar yarinya da harsashi ya samu a goshi sakamakon buɗe wutar da maharan suka yi, amma tana nan a asibiti ana yi mata magani.

Akwai kuma mota guda daya da ake kyautata da ‘yan Boko Haram ne da aka gani ta kone ƙurmus da mutane biyu a ciki, in ji kakakin rundunar ƴan sandan, kana akwai motar hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa NCDC da mayakan suka yi awon gaba da ita.

 

Me mazauna garin na Gaidam ke cewa?

Daya daga cikin mazauna yankin da BBC ta tattauna da su ya bayyana cewa tun daga misalin ƙarfe biyar na yamma da suka shiga garin ba su fita ba har sai misalin ƙarfe uku na dare.

”Har da misalin ƙarfe goma sha biyun dare ma muna cikin gida mun riƙa jin harbe-harbe – sun je cikin asibiti suka ɗebi magunguna, kana a kan kwanar asiitin kuma suka fasa wani shagon sayar da magani suka sake kwasar magunguna,” ya ce.

Kana sun ƙona gidan tsohon shugaban ƙaramar hukumar ta Gaidam, suka ƙona wasu shaguna a kusa da wurin,” sun kuma yi awon gaba da hakimin Ma-Gana.

‘Yan Boko Haram din in ji mazaunin garin, sun shigo a kan motoci ne amma sun karkasa kansu ne wurare daban-daban.

”Motocin da suka shigo a cikin za su kai wajen guda bakwai, kuma ko wace mota tana dauke da mayaƙan aƙalla 20, da galibinsu ƙananan yara ne wallahi,” in ji shi.

Ba su shiga cikin kasuwa ba, amma sun kwashi kaya ne a bakin kasuwa, sannan suka ƙona wasu shaguna a bakin kasuwar.

”Sun kwashi magunguna da kayan abinci masu dama, amma ba su kashe ko jikkata kowa ba,” ya yi ƙarin bayani”.

Daya mazaunin garin na Gaidam shi ma ya shaida wa BBC cewa mayaƙan sun shigo musu gari babu zato babu tsammani ne, kuma duk da cewa ba su jikkata ko kashe kowa ba, amma sun shiga halin fargaba.

”Muna cikin harkokinmu ne da yake ranar kasuwar garin ne, sai kawai suka kawo farmaki suka tayar da hankulan jama’a da kone-kone da harbe-harbe, amma dai yanzu mun cigaba da harkokinmu,” ya ce.

Rundunar ƴan sandan jihar Yobe ta ce yanzu haka jami’an tsaro na nan na ta sintiri a cikin garin na Gaidam, yayin da jama’a suka fito suka ci gaba da harkokin nasu.

Mayakan Boko Haram din dai na ci gaba da kai faramaki a yankuna daban-daban a jihohin na Borno da Yobe masu maƙwabtaka da juna, duk kuwa da ikirarin da hukumomin tsaron kasar ke yi na cewa suna samun galaba a kansu.

 

Tushe: BBC Hausa

Leave a Reply