www.sautizallah.com
Legit - Purevybz Pressplay

FASSARAR LITTAFIN “KITAB FASL AL-MAQAL (DAIDAITO TSAKANIN FALSAFA DA ADDINI)
NA IBN RUSHDI

0
“KITAB FASL AL-MAQAL”

KASHI NA FARKO
 
GABATARWA
Asalin Kalmar Falsafa ta samo asali ne daga yaren Girkawa wadda ke nufin “Son hikima”. Wani masani wanda ake kira Phythagoras (wanda mu ke karantawa a fannin lissafi mai phythagoras theorem) wanda ya rayu kimanin shekaru dari 600 kafin zuwan annabi Isa, shine ya fara amfani da wannan kalma ta falsafa.
Masana wannan fanni sun karkasa Falsafa zuwa bangarori guda shida.


i) Metaphysics:-Sashen da ya kunshi menene ma’anar Hakika? Wato idan aka ce hakika me ake nufi, shin ya jibanci abu guda ne ko kuma ya kunshi abubuwa ne? shin hanyoyin sadarwa da Allah ya huwace mana (Ji, gani, dandana, shaka da Tabawa) na iya tsinkayar ita hakika ko kuwa sai dai ruhi ne ke iya tsinkayarta?
ii) Epistemology:-Sashen da ya shafi ilimi, menene ilimi? Me ake nufi da sani? Yaya ake samun ilimi?
iii)Value-theory:-Nazarin kimar abubuwa. Me ake nufi da kimar abu? Wadanne ire-iren kima ake da su?
iv)Ethics:- Mu’amala mai kyau (Morality) yaya take, mecece ita? Ya ta ke dangantaka da aiki, nufi, aiwatarwa da dangataka tsakanin halittu?
v) Aesthetic:- Fasaha da yadda kyau yake. Menene fasaha kuma menene abu mai kyaun siffa? Menene dangantakar fasaha da hakika da gaskiya?
vi) Logic:- Hanyar da ake tsefe tunani domin cikakkiyar fahimta. Ta wannan hanya masu nazarin falsafa ke amfani da tunani don yin bincike ko nazari domin fahimtar abubuwa
 
Masana falsafa na amfani da hanyar zuzzurfan tunani don bayanin abubuwa ta yadda za’a fahimta cewa akwai hankali cikin Magana tare da bada kwararan hujjoji.
 
“Al’ajabi…shine abinda ya saka a tun farkon zamani har zuwa yanzu mutane ke bin tsarin falsafa” In ji Aristotle
 
Akwai Falsafa ta kimiyya, da falsafar ilimi, da ta addini, falsafar shari’a, ta fasaha da sauransu. Hanyoyin da ake bi don yin falsafanci sun dogara ko kuma suna farawa daga batutuwa guda uku.

–  Babu wata Magana da za’a ce haka take kuma ba haka ta ke ba, a lokaci guda kuma a yanayi guda
–  Duk abinda za’a ce, ko dai haka ya ke ko kuma ba haka yake ba
–  Duk wani abu na kasancewa ne a yadda ya ke
A takaice wannan bayani shine abinda ake nufi da falsafa.

Idan mu ka juyo bangaren musulunci, wanda ya fara nazarin falsafa shine Al-Kindi a farkon karni na 9 (wato karnin na 2 bayan hijira) kuma ya kai tsaiko tare da Ibn Rushid a karni na 12 (karni na biyar bayan hijira) kafin a murkushe shi da karfin tsiya, koda yake ya dan farfado kadan a yankunan Farisa, Ottoman da daular Mughal ta indiya. Sai kuma kokari na baya-bayan nan a karni na 19 da na 20 karkashin yunkurin “Nahda” wato farkawa, wadda shaihun malami Tantawi a misra karkashin mulkin Muhammad Ali ya yi kokarin farfado da falsafanci a duniyar musulmi.  Idan mu ka koma can baya a tarihi game da nazarin falsafanci, ya kamata mu fara fahimtar mecece falsafa a shari’ance yadda Qur’ani da hadisi su ka nuna, kuma magabata suka dauka suka habaka. Da farko a musulunce kamar yadda muka gani a baya, falsafanci ya samo alaka ne daga kalmar Hikima, wadda Allah ya yi bayanin ta a wurare 20 cikin Qur’ani, cikin wadannan wurare, guda daya yawanci malamai su ke fassarawa don dangantawa da falsafanci wato:
Q2:269 “Ya na bada hikima ga wanda ya so, kuma wanda aka baiwa hikima, hakika ya sami babban rabo”
A cikin hadisi kuma Annabi ya ce “Neman hikima wajibi ne a kan ku, hakika alhairai na cikin hikima” sannan kuma ya ce “Kada ku yi maganar hikima ga wawaye”. Malamai magabata sun fassara falsafar musulunci, misali Al-Kindi cewa ya yi “Falsafa ilimin hakikar abubuwa ne gwargwadon fahimtar dan Adam, domin burin masanin falsafa shine ya fahimci menene gaskiya kuma ya yi kokarin aikata ta cikin rayuwarsa” wannan fassara ita ma Al Farabi ya bi. Shi kuma Ibn Sina cewa ya yi “Hikima ita ce cikar ruhin dan adam ta hanyar tsinkayen abubuwa da kuma bada hukuncin ilimi da aikin gaskiya a zahiri don auna irin ikon mutum”. Su kuma Ikhwan al-Safa cewa su ka yi “Farkon falsafa shine son kimiyya, tsakiyarta shine sanin ilimin hakika da iya ikon mutum, karshenta kuma shine furuci da aiki wanda ya dace da ilimin da aka sani”. Mullå Sadrå shi kuma sai ya ce: “Hikimar falsafa ita ce wadda annabi ke nufi lokacin da ya ce cikin addu’arsa “Ya ubangiji ka nuna mana abubuwa (mu fahimci) yadda su ke a hakika” wato samun yakini ke nan.
Fantsamar musulunci a kasashen waje ya baiwa musulmi damar cudanya da sauran al’ummomi da ilime-ilimensu, musamman a Andalusiya inda musulunci ya kafa babbar daula a gabar yankin kasashen turai. Hangen nesa na malamai a wancan zamani ya saka an fara fassara littafai na al’ummomin baya da su ka yi rubutu musamman daga Girka. Alaka ta farko tsakanin falsafanci da musulunci ta wanzu sakamakon fassara rubuce-rubuce, musamman na Aristotle. Falsafa ta bada gagarumar dama ga masanan wannan fanni na farko a musulunci domin sun yi amfani da ita wajen wannan fassara wadda ta habaka harkar kimiyya a wancan zamani inda daga karshe musulmi suka karbe matsayin ja-gaba wajen nazari da binciken kimiyya a duniya.
Bayyanar Al-Ghazali a matsayin babban malamin musulunci wanda ya fara yaki da malaman falsafa na musulunci irinsu Ibn Sina da Al Farabi ya kawo cikas ga habakar wannan fanni a musulunci, abinda ya kai ga gurguntawa da canza akalar yadda musulmi su ka dauki falsafa tun daga wancan lokaci zuwa yanzu. Abin da ya kamata a yi la’akari da shi shine cewa ba kasancewar hujjojin Al-Ghazali sun shafe na wadancan masana falsafa ba ne, ko alama, amma kasancewar mafi yawan mutane ba su da ilimi don haka mahangarsu gajera ce, shi kuma ilimin falsafa da su Ibn Sina da Ibn Rushidi ke kokarin yadawa ya zarce kwakwalwar mutanen zamaninsu. Wannan ya sa mafi yawan mutane su ka raja’a ga Al-Ghazali wanda ta haka aka murkushe karsashin falsafanci a duniyar musulmi. Akasarin mutane na kallon Ghazali a matsayin tauraro (har lakabin Hujjatul-al-islam aka ba shi) amma a zahiri rawar da ya taka, ta dakile al’ummar musulmi tun daga wancan zamani kawo yanzu. A cikin wannan littafi da na fassara, mai karatu zai ga inda shi kansa Al-Ghazali ya ke kifirta wadancan malamai saboda abubuwan da su ke fada wanda ya kasa fahimtar su yadda zai yarda da su. Daga nan ne Al-Ghazali ya assasa rigimar da har yanzu take mana zagon kasa a musulunci domin duk wani wanda bai yarda da akidar ka ba sai kawai ya nemi fitar da kai daga addinin gaba daya.
Daga baya an yi kokari a wurare da lokatai daban daban domin ganin cewa an dawo da falsafa cikin tsarin ilimin jami’o’in musulunci musamman wanda aka yi a Baitul-Hikma ta Bagadaza da kuma Jami’ar Azhar lokacin Fatimid amma kuma a yawancin makarantu da ke karkashin mulkin Abbasid da Seljuq an haramta koyar da falsafa gaba daya.
Babu wata al’umma a duniya wadda ta yi fice kama daga Akadiyawa, Sumeriyawa, Girkawa, daular Pasha, Sinawa, Japanawa da Turawa wadanda suka yarda da kore falsafa daga tsarin zamantakewarsu. Duk da cewa kowacce al’umma na da tata falsafar babu wadda ta tsaya ga tsarinta shi kadai, face ta yi aro daga wasu al’ummomi domin ingantawa da kyautata ta. Kowacce al’umma a yau na tafiya da tsarin falsafancinta banda musulmi, kasancewar mafiya yawan mabiya a musulunci sun fada bangaren ‘yan sunna ko ‘yan shi’a, kuma an gina ilimi na wadannan bangarori, misali sunna sun riki “Salaf” yadda duk wani abu da ya zo sabani da su a kan yi watsi da shi (wasu ma cikinsu na da imanin cewa an rufe kofar ijtihadi), haka nan ‘yan shi’a sun yi riko da imamai wadanda su kadai ke bada mahanga. Wannan tsari shi ya kashe, murus, fannin falsafanci kuma ya jawowa musulmi mummunar asarar basirar dubban mutane masu hikima wadanda da an tarbiyantar da su a tsarin falsafanci da sun samarwa al’ummar mafita mai yawa daga matsalolinsu. Dole kowanne zamani ya sami malamai wadanda za su rika nazari na nassi tare da fitar da ma’anoni na ayoyin Qur’ani sakamakon ilimin zamani da ya samu.
A karshe ya kamata mu fahimci cewa a tarihin musulunci, a bangaren ci gaba, babu wani abu da ya kawo habaka da daular musulunci ta yi fiye da karbar falsafa, tsakankanin karni na 9-12, wadda ta bata damar nazarin kimiyya da fasahar mutanen da suka gabace ta, kuma ta dora harsashin da a yanzu ya zama kashin bayan ci gaban zamani da turawa ke jagora. Matukar musulmi na son su sake samun damar taka rawa ta gaske a zamantakewa, ilimi, siyasa da tattalin arziki na duniya wajibi ne mu koyi wancan tsari da su Ibn Sina, Ibn Rushidi da Al-Farabi suka gina wanda turawa suka kwashi garabasarsa. Matukar zamu ci gaba da riko da tunani irin na su Al-Ghazali wanda shine tsiron da ya haifar malamai suka bada fatawar rufe kokofin ijtihadi, hakika zamu ci gaba da zama a kurar baya a fannin ilimi, wanda shine jagoran ci gaban kowacce irin al’umma.

TATTAUNAWA DON GANO IRIN ALAKAR DA KE
TSAKANIN ADDINI DA FALSAFA

YAYA SHARI’A KE KALLON FALSAFA?
Shehun malami, likita, Alkali masanin shari’a, Abul Walid Muhammad Ibn Ahmad Ibn Rushid ya ce: “Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda ya cancanci dukkan yabo, Da addu’a ga Annabi Muhammadu, zababbensa, bawansa kuma manzonsa. Dalilin wannan tattaunawa shine domin nazari, daga mahanga ta shari’a, don tantancewa shin karatun ilimin falsafa (Philosophy) ya halatta a shari’ance ko kuwa haramun ne ko kuma an umarci da ayi a shawarce ko kuma a matsayin wajibi ya ke”
 
BABI NA DAYA
 
SHARI’A TA WAJABTA KARATUN ILIMIN FALSAFA
 
“Idan har nazarin yadda duniya ta ke falsafa ne, kuma idan har shari’a ta umarci a yi wannan nazari, don haka shari’a ta yi umarnin a yi nazarin falsafa”
 
Idan mu ka ce: Idan har nazarin falsafa bai wuce nazarin halittu da su ka wanzu ba da kuma yin tunani a kan su da kuma ayyukan da ke nuna fasahar yin su, wato abinda ke nuna fasahar (domin halittu na nuna fasahar yadda aka yi su ta hanyar iliminmu na fasahar da ke kunshe cikinsu ta yadda karuwar wannan ilimi na mu na fasahar da aka yi su, na kara mana sanin mai fasahar da ya yi su) to idan har shari’a ta bamu kwarin gwiwa da azamar mu yi tunani a kan halittu, a bayyane ya ke cewa nazarin falsafa wajibi ne ko kuma abinda shari’a ta assasa a yi.

SHARI’A TA UMARCI A YI NAZARIN FALSAFA
 
Shari’a ta nemi da a yi tunani a kan halittu, kuma da neman ilimi a game da su, wannan ya bayyana karara daga ayoyin littafin Allah mai tsarki, kamar fadarsa mai tsarki “Ku yi tunani, an baku gannai” wannan hujja ce da ta wajabta amfani da basira ko kuma yin amfani da basira da shari’a. Wani misalin shine a cewarsa “Shin ba ku duba mulkin sammai da kasa ba, da kuma abubuwan da Allah ya halitta?” wannan aya na neman a yi nazarin dukkan abin halitta. Haka nan Allah madaukakin sarki ya sanar da mu cewa cikin manyan bayinsa da ya daukaka shine Ibrahimu, aminci ya tabbata a gare shi, Allah ya ce “Mun baiwa Ibrahimu ilimin sammai da kasa, domin ya kasance…”(har karshen ayar). Madaukakin sarkin ya ce “Shin ba ku ga yadda muka halitta rakumi ba, da sammai yadda muka daukaka ta?” sannan ya ce “Su na duba yadda ya halicci sammai da kasa” da wasu sauran ayoyi masu tarin yawa irin wadannan.
 

DOLE A YI WANNAN NAZARI CIKIN NATSUWA TA HANYAR KAFA HUJJOJI BAYYANANNU
 
Tun da mun tabbatar da cewa shari’a ta wajabta nazarin halittu ta hanyar yin tunani da basira don fahimta, kuma tunda shi tunani da basira don fahimta ba wani abu ba ne illa zakulo abinda ba’a sani ba daga abinda ka sani, kuma tun da haka shine tunani na fahimta ko tunani don fahimta, don haka wajibi ne mu ci gaba da nazarin halittu ta hanyar tunani da basira. A fili ya ke cewa wannan hanya ta nazari, wadda shari’a ta umarce mu, hanya ce da ta fi kowacce wajen nazari ta yin amfani da mafi kyawon tunani wanda shi za mu kira “Bada hujja ta zahiri”
 
Domin nakaltar wannan dole ne malamai na addini su yi amfani da koyon nazarin tsefe tunani (logic) kamar yadda ya wajaba akan Masanin shari’a ya nemi sanin ilimin amfani da basira na shari’a. Babu abinda ya haramta wannan ko wancan. Kuma dole ne a koyi ilimin tsefe tunani daga masanan farko, ko da sun kasance musulmi ko ba musulmi ba.
 
Shari’a ta azama mu domin neman ilimin Ubangiji da halittunsa ta hanyar hujjoji bayyanannu. Amma an fi so, ko kuma ya fi zama wajibi ga duk wanda ke son ya fahimci Allah madaukaki da sauran halittu ta hanyar hujjoji bayyanannu, ya fara samun fahimtar yaya hujjoji bayyanannu su ke, kuma ta ina suka banbanta da sauran hujjoji. Hakan ba zai samu ba sai fa idan mutum ya san yaya tunani da basira ya ke, kuma iri nawa ne, kuma wanne ne karbabbe wanne ne ba karbabbe ba. Wannan ba zai samu ba shima har . sai an san yaya tunani na basira ya ke, da abubuwan da ya kunsa. Don haka wanda ya yarda da shari’a, ya ke biyayya gareta don nazarin halittu, ya fara da nazarin ilimin abubuwan, wadanda ke da mazauni guda a ilimance ko a zahirance.
Kamar yadda Masanin shari’a, sai ya san sassa na alkalanci wadanda suke karbabbu da sabanin haka… kafin ya iya tace kalmomin Allah don zakulo fannoni na shari’a, haka shi ma mai neman sanin (Ubangiji) sai ya san yadda ake tunani da basira da fannoninsa kafin ya iya tacewa don zakulowa daga umarnin Allah cewa nazarin halitta wajibi ne. Ya ma fi cancanta fiye da alkalai, domin shi Masanin shari’a idan ya fahimta daga fadar Allah cewa “Ku yi nazari, ya ku masu idanuwa” wato  ya yi nazarin zakulo hukunci, yaya kuma ga malami wanda ke son ya fahimci ubangiji daga wajabcin samun ilimi da amfani da tunani na basira? Ba za’a yi suka da cewa “Irin wannan nazari na tunani da basira bidi’a ce ba, domin sahabban farko ba su yi ba” Domin a hakika sahabban farko su ne suka fara irin wannan nazari na tunani da basira wajen kafa hujjoji ko zakulo hukunci na shari’a, amma ba a dauki wannan fanni bidi’a ba. Don haka mai wannan suka sai ya yarda da cewa irin wancan
tunani (na falsafa) tamkar na zakulo hukunci daga shari’a ne. Yawancin malaman musulunci sun yarda da tunani na basira, banda wasu kalilan da ke son su bi hukunce-hukunce na zahiri, wadanda za’a iya yiwa raddi kai tsaye daga Qur’ani da hadisi.

Daga Ali Abubakar Sadiq

Kindly follow our social handles below for latest update and more;

Facebook Page: @Sautizallah
Instagram: @Sautizallah
YouTube: Sautizallah TV
Twitter: @Sautizallah

Thanks

Leave a Reply