Labarai

Solomon Dalung: Jam’iyyar APC na tangal-tangal

Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Mista Solomon Dalung, wanda tsohon minista ne a gwamnatin, ya ce APC ta gaza wajen cika alkawuran da ta yi wa ƴan ƙasar.

Mista Dalung ya shaida hakan a hirar da aka yi da shi ya ce batun inganta tsaro shi ne babban alkawarin da jam’iyyar ta yi wa ƴan Najeriya, amma yadda tsaro ya tabarbare, musamman ma a arewacin ƙasar, APC ba ta da kyakkyawar makoma, kuma ba ta da idon da za ta kalli jama’ar kasar da shi.

Ya ce matsalar ta tsaro ta jefa rayuwar jama’a cikin zulumi da tsoro saboda yin tafiya cikin Arewa a halin da ake ciki ta zama tashin hankali saboda dole ne sai mutane sun haɗa da addu’a da kuma azumi.

“A ce wai a Arewa wai kafin ka yi noma sai ka biya ɗan bindiga kuɗi, idan ka gama noman ka biya shi kuɗi kafin ka zo ka yi girbi, ina ma ke nan maganan noma a Arewa?”, in ji tsohon ministan.

A ganinsa, ba a taɓa shiga irin wannan yanayi ba saboda “gwamnatin nan da muka kafa, ba ta biya wa ƴan Najeriya buƙata ba, gwamnatinmu ce amma yanzu idan ba mu yi dai-dai ba, haƙƙinmu ne mu fita mu faɗa domin mun yi wa wasu jiya, saboda haka sai mu yi wa kanmu yau”.

Jam’iyyar APC na cikin garari…

A cewar Solomon Dalung, APC ba ta da wata makoma saboda “a yanzu an rushe jam’iyyar baki ɗaya, ba ta da mambobi – ko shugaban ƙasa ma ba mamba bane”.

Ya ce “mu yanzu ma ba ƴan APC bane, sai an dawo mana da takarda mun sake shiga jam’iyya kamar shigar soja”.

Tsohon ministan ya soki matakin kafa kwamatocin riƙo inda ya ce “ba za ka tashi yau saboda gidanka na yoyo ka kawo katafila ka rushe gidan a koma a yi sabon gini”.

A halin yanzu, ya ce shi tsohon ɗan APC ne domin yana jira ne a sake buɗe ƙofa sai ya shiga.

Tushe: BBC Hausa

Kindly follow our social handles below for latest update and more;

Facebook Page: @Sautizallah
Instagram: @Sautizallah
YouTube: Sautizallah TV
Twitter: @Sautizallah

Thanks

Leave a Reply