Insecurity Labarai Politics

Nijar ta amince ta taimaka wa Chadi wajen yaƙi da ƴan tawaye

Jamhuriyar Nijar ta amince da buƙatar Chadi ta neman agaji kan ƙungiyar ƴan tawaye ta Front for Change and Concord in Chad (FACT), wadda ake zargi da kashe Shugaba Idriss Deby ranar Litinin, kamar yadda gidan radion Faransa, RFI ya ruwaito.

“A cewar wata majiya, a yau Nijar ta ba wa Chadi cikakken haɗin kai,” a cewar majiyar.

Haka kuma, ta ce rundunonin tsaron ƙasashen biyu na aiki tare a ko da yaushe kuma kawo yanzu an kama wasu ƴan tawayen a Dirkou, yankin Agadez.

Wannan matakin na zuwa ne duk da sa bakin da Shugaban Nijar, Mohamed Bazoum ya yi a rikicin Chadi yayin taron ƙoli na G5 Sahel da aka gudanar ba shiri daf da lokacin jana’izar Idriss Deby.

RFI ta ce “Wasu na tambaya shin Nijar, wadda ta kasance mai shiga tsakani a rikicin, ta ɗauki ɓangare ne ta hanyar amincewa da buƙatar Chadi?”

Wasu na ganin hakan ne kuma Nijar a ashirye ta ke ta tsaya da Chadi tunda duka ƙasashen biyu na G5 Sahel ne.

Majalisar Soji ta riƙo a Chadi ta ƙi amincewa da sulhu ko tattaunawa da FACT kuma ta ce mayaƙan ƙungiyar sun tsere zuwa nIjar bayan da suka fuskanci yaƙi mai tsauri a karawar da suka yi da marigayi Idriss Deby ya rasa ransa.

Tushe: BBC Hausa

Subscribe
YouTube @SautizallahTV 🤲
Read || ReBroadcast || Share 🙏

Leave a Reply