Africa Insecurity News Politics

Rikici ya barke tsakanin sojojin Chadi da ‘yan tawaye a kasar

Dakarun gwamnatin Chadi sun kaddamar da farmaki kan ‘yan tawayen kungiyar FACT a garin Nokou da ke cikin lardin Kanem da ke yammacin kasar, inda bayanai ke cewa an samu mummunar asara a wannan artabu.

Kakakin gwamnatin mulkin sojin kasar Janar Azem Bermandoa Agouna ya sanar da haka, inda ya ke cewa ana can ana fafatawa a Kanem.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce majiyoyin sun shaida masa cewar sojojin gwamnati sun kai harin sama kan dakarun ‘yan tawayen FACT a ranar Talata, kuma ana gwabzawa ne a wurin da ke da nisar kilomita 300 daga birnin N’Djamena.

Kakakin Majlisar mulkin sojojin kasar Janar Azem Bernandao Angouna, ya ce kaddamar da farmaki kan ‘yan tawaye wadanda suka kashe shugaban Idris Deby ya zama wajibi domin hana su wargaza kasar ta Chadi.

Shi dai lardin Kanem, yana da tazarar akalla kilomita 300 daga birnin Ndjamena, inda ‘yan tawayen suka ja daga bayan tsagaita wuta kwana daya bayan kashe Marshal Idris Deby, yayin da wasu bayanai ke cewa sauran ‘yan tawayen sun tsallaka iyaka don samun mafaka a cikin jamhuriyar Nijar.

Wata majiyar soji kuwa, ta bayyana cewa ‘yan tawayen sun yi nasarar harbo jirgi mai saukar angulu na rundunar sojin kasar ta Chadi a kusa da garin Nokou a ranar Alhamis.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake dakon isar tawagar kungiyar Tarayyar Afrika a birnin Ndjamena, wadda za ta kasance karkashin jagorancin Bankole Adeoye, sabon shugaban kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar, sai kuma Mohamed Idris Farah dan Djibouti kasar da ke jagorantar kwamitin tsaro na kungiyar ta AU.

Tushe: RFI Hausa

Subscribe
YouTube @SautizallahTV 🤲
Read || ReBroadcast || Share 🙏

Leave a Reply