Labarai

Saudiyya: Ana shigar da kwayoyi daga Lebanon da sunan kayan marmari

Hukumomin Lebanon sun ce suna fatan kasar Saudiyya za ta dage haramcin da ta sanya na shigar da kayan lambun da na marmari da ta ke shiga da su kasar.

Gwamnatin Saudiyyar ta ce ana fakewa da shigar da kayan wajen yin fasa kwaurin muggan kwayoyi, tare da zargin hukumomin Labanon da kin daukar matakin da ya dace.

Sanarwar da gwamnatin Lebanon ta fitar, ta ce an shaidawa ministan cikin gida Muhammad Fahmi ya yi aiki tare da hukumomin saudiyya domin bankado masu wanna aika-aika tare da daukar matakin kar hakan ta sake faruwa.

Wannan mataki na Saudiyya dai zai kara dagula lamura da janyo koma bayan tattalin arziki ga Lebanon, wanda tuntuni yake faman tangal-tangal.

Tushe: BBC Hausa

Subscribe Now
YouTube @SautizallahTV 🤲
Visit www.sautizallah.com
Read || ReBroadcast || Share 🙏

Leave a Reply