Africa

Shugaban Chadi ya yi alƙawarin tattaunawa da duka ɓangarorin ƙasar

Mahamat “Kaka” Déby Itno Shugaban Sojojin Tchadi

Sabon jagora a Chadi Mahamat “Kaka” Déby Itno, ya gabatar da jawabi ga ƴan ƙasar inda ya yi alƙawarin tattaunawa da kowane ɓangare na ƙasar domin maido da gwamnatin farar hula cikin wata 18 bayan kusan mahaifinsa kuma daɗaɗɗen shugaban ƙasar Idris Déby.

Sabon shugaban ya kuma yi alƙawarin yaƙi da ta’addanci.

Jawabinsa na zuwa ne yayin da jama’ar ƙasar ke zanga-zanga kan yadda sojoji suka karɓe ragama a babban birnin ƙasar da Moundo da ke Kudancin ƙasar.

Kimanin mutum biyu ne suka mutu a rikicin.

Tushe: BBC Hausa

Subscribe
YouTube @SautizallahTV 🤲
Read || ReBroadcast || Share 🙏

Leave a Reply