Africa

Shugaban Faransa ya yi tur da rikicin Chadi

Shugaban Faransa Emmanuel Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ta yi tur da rikicin baya-bayan nan da ya ɓarke a Chadi inda ya yi kira da a miƙa mulki ga gwamnatin dimokradiyya cikin lumana.

Kimanin mutum biyu ne aka bayyana sun mutu yayin da jami’an tsaro suka yi arangama da masu zanga-zanga da suka fusata da yadda sojoji suka karɓe mulkin ƙasar.

Rahotanni na cewa ƴan sanda sun harbe wani matashi ɗan shekara 20 a birnin Moundou.

A babban birnin ƙasar, N’Djamena, ƴan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar da suka ƙona tayoyi a wurare da dama.

Bayanai na cewa sama da mutum 20 sun jikkata sakamakon rikicin.

Tushe: BBC Hausa

Subscribe
YouTube @SautizallahTV 🤲
Read || ReBroadcast || Share 🙏

Leave a Reply