Babban Labari

Sojojin Najeriya sun haramta zirga-zirga a hanyar Damaturu

Sojojin Najeriya sun hana zirga-zirga a hanyar Damaturu-Damboa-Biu bayan hare-haren da mayaƙan ƙungiyar ISWAP/Boko Haram suka kai kan sansanin soji da ke Kumuya a jihar Yobe.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta tattaro bayyanan da ke cewa “ƴan ta’adda sun kai hari a lokacin da sojojin da aka girke a Buni Gari suka tafi aikin sintiri”.

‘Yan ta’addan wadanda wasu suka taimaka musu da bayanai sun kutsa kai cikin yankin na Kumuya, tare da afkawa ƙauyuka da sansanin sojoji kuma suka lalata kayan aikin jami’an tsaro masu tarin yawa.

Rahotanni sun ce mayakan sun yi amfani da manyan makamai wajen lalata kayan sojoji tare da yin sintiri a cikin al’umma don hana sojoji sake ƙarfafa kansu.

Sai dai duk da haka, sojojin da ke kasa sun zo sun yi artabu da su.

Daga karshe sojojin Najeriya da suka hada ƙarfi da ƙarfe sun fatattaki maharan.

Duk da cewa an samu labarin cewa wani ɓangare na sansanin sojoji da ke Kumuya ya kone yayin harin, amma kafar watsa labarai ta PRNigeria ba ta iya tabbatar da adadin sojojin da suka hallaka ba.

Leave a Reply