Labarai

’Yan Bindiga Sun Kona Motar ‘Yan Banga

Ana fargabar cewa wasu ’yan bindiga sun kone wata motar sintiri ta ‘yan banga a kan babbar hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

Jagoran ’yan banga a yankin, Udawa Muhammad Umar ya tabbatar wa da Aminiya faruwar lamarin wanda ya auku da misalin karfe 4.30 na Yammacin ranar Juma’a yayin da ’yan Bandar ke bakin aikinsu.

Sai dai ya ce an yi sa’a babu wanda ya ji rauni kuma babu rai ko daya da ya salawanta a yayin harin.

Udawa wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ya auku ne a kusa da babbar hanyar Baruku zuwa Udawa a wani wuri da ake kira Unguwar Yako a babbar hanyar ta Kaduna zuwa Birnin Gwari mai hatsarin gaske.

Ya ce, “harin ya faru ne a lokacin da jami’anmu ke sintiri a kan babbar hanyar, inda aka rika musayar wuta tsakaninsu da ’yan bindigar, amma ’yan ta’addan sun samu nasarar kona motarmu daya rak da ta rage kirar Golf wacce muke aikin sintiri da ita,” inji shi.

A cewarsa, babu wani dan banga ko daya da aka kashe yayin harin, sai dai ya bukaci gwamnati ta kawo musu tallafin wata motar.

Aminiya ta tabbatar da cewa motar da aka kona ita kadai ce wacce ta rage wa ’yan bangar da suke samu suna gudanar da ayyukansu na sintiri a kan babbar hanyar.

A kwanan baya ne aka yi wani mummunan hatsari da daya motar ‘yan bangar wanda ya yi ajalin mutum 14 yayin da dama suka jikkata inda a halin yanzu ake jinyarsu a Asibitin Birnin Gwari.

Yayin da aka tuntubi jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya ce ba a sanar da shi a hukumance ba, sai dai ya ce zai tuntubi jami’an ‘yan sandan yankin inda ya har yanzu lokacin hada wannan rahoto bai waiwayi manema labaran da suka nemi jin ta bakinsa ba.

Tushe: Aminiya
Kindly follow our social handles below for latest update and more;

Facebook Page: @Sautizallah
Instagram: @Sautizallah
YouTube: Sautizallah TV
Twitter: @Sautizallah

Thanks

Leave a Reply