Africa Babban Labari

Yariman Saudiyya ya zanta da Mahamat Idriss Deby

Mahamat Idris Deby Shugaban Sojojin Kasar Tchadi

Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman bin Abdulaziz da mataimakin Firaminista da kuma ministan tsarp sun tattauna da shugaban sojin Chadi Mahamat Idriss Deby. Ta wayar tarho a ranar Lahadi.

Kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya ce Yarima bin Salman ya yi wa Janar Mahamat Deby ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa Idriss Deby wanda ya rasu a ranar Litinin sakamakon samun raunika a fagen daga.

Yariman ya yi wa Chadi fatan ɗorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A nasa ɓangaren kuma Janar Mahamat ya gode wa Yariman kan karamcin da ya nuna masa.

Tushe: SPA Saudi Da BBC Hausa

Subscribe Now
YouTube @SautizallahTV 🤲
Visit www.sautizallah.com
Read || ReBroadcast || Share 🙏

Leave a Reply